Plateau: Matar da ƴanbindiga su ka sace ta haihu a hannun su
Wata matar aure da aka sace tare da ‘yarta a yankin Kyaram da ke gundumar Garga a ƙaramar hukumar Kanam ta jihar Plateau ta haifi jariri yayin da take a hannun masu garkuwa da mutane.
’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 a Jihar Filato
An Saki Sauran Ɗaliban Makarantar KatoliKa 130 Da Aka Sace A Neja
Faɗa ya kaure tsakanin jami’an soji da na ‘yansanda a garin jos jihar Filato.
Masu garkuwan sun kashe mijinta, Umar Rufa’i, kafin su sace ta tare da ‘yarsu.
Sakataren ƙungiyar ci gaban Kanam (KADA), Shehu Kanam, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa masu garkuwan sun kira iyalan mamacin suka sanar da haihuwar.
Ƙungiyar ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin mummunan aiki, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin da al’ummar Kyaram.
KADA ta kuma nuna damuwa kan yawaitar sace-sace da hare-haren ‘yan fashi a gundumar Garga, tana kiran gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.
Rundunar ‘yansandan jihar ba ta ce komai kan lamarin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.









