Home Afrika Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai jagoranci shari’a kan kisan matar...

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai jagoranci shari’a kan kisan matar aure da ‘ya’yanta shida a Dorayi

90
0

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai jagoranci shari’a kan kisan matar aure da ‘ya’yanta shida a Dorayi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano.

Babu Tabbas Kan Ranar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Zai Koma Jam’iyyar APC

Saudiyya Ta Zartar da Hukuncin Kisa Kan Mutane 347 A 2025

Kotun Bangladesh ta yanke tsohuwar Firaminista Hasina hukuncin kisa

Gwamnatin ta bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin tausayi da imani, wanda ya girgiza al’ummar jihar tare da zama cin zarafi ga bil’adama da doka.

A cikin wata sanarwa da babban lauyan jihar Kano kuma kwamishinan shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya fitar, ya ce bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da daukacin al’ummar Kano.

Sanarwar ta ce gwamnati na tare da iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa ba za a barsu su kaɗai ba a wannan mawuyacin lokaci.

Gwamnatin ta kuma yaba wa rundunar ‘yansandan jihar bisa gaggawar ɗaukar matakan bincike da suka kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin, tana mai cewa hakan na nuna ƙudirin hukumomin tsaro na tunkarar aikata laifuka da dawo da amincewar jama’a.

Ta jaddada cewa za a gudanar da shari’ar cikin gaggawa da ƙwarewa ta hannun ofishin babban lauyan jihar, inda za a kafa tawagar lauyoyi ta musamman domin tabbatar da adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   9   =