Home KASUWANCI NAFDAC ta ƙwace miliyoyin magungunan zazzaɓin cizon sauro na Bogi

NAFDAC ta ƙwace miliyoyin magungunan zazzaɓin cizon sauro na Bogi

79
0

NAFDAC ta ƙwace miliyoyin magungunan zazzaɓin cizon sauro na Bogi

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa, NAFDAC, ta ƙwace sama da magungunan zazzaɓin cizon sauro na bogi miliyan 10 tare da kayan kwalliya, waɗanda kimarsu ta kai kusan naira biliyan uku, a wani farmaki da ta kai kasuwar baje koli da ke jihar Lagos.

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano Ta Amince da Mayar da Ragowar Kuɗi ga Maniyatan Hajjin 2026

UNICEF Ta Jinjinawa Gwamnan Kano A Bisa Kula Da Kananan Yara

Matatar Ɗangote Ta Ƙayyade Farashin Litar Fetur Zuwa N739

  1. Daraktan bincike da aiwatar da doka na NAFDAC, Dr Martins Iluyomade, ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin hukumar da ke Apapa a ranar Litinin.

Ya ce an kai farmakin ne ƙarƙashin jagorancin shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 3 ga Fabrairu.

A cewarsa, kayan da aka ƙwace sun haɗa da magungunan yaƙi da zazzaɓin cizon sauro da alluran cutar cerebral malaria da magungunan rigakafi da maganin tazarar haihuwa na Postinor, da Anagin kuma duk na bogi.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗannan magunguna an haramta amfani da su a Najeriya kusan shekaru 15 da suka wuce.

Daraktan ya ce an adana magungunan bogin ne a wani gini mai hawa uku da aka ɓoye shi a matsayin sito na kayan gyaran mota, domin yaudarar jami’an tsaro da hukumomi.

A yayin farmakin, an kwashe lodin manyan motoci guda takwas na magunguna da kayan kwalliya, tare da kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a lamarin.

Daraktan ya ce bincike na ci gaba da gudana, inda ya bayyana farmakin a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da hukumar NAFDAC ta samu a baya-bayan nan wajen yaƙi da magungunan bogi a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   5   =