Aƙalla sojoji biyu da ’yan sanda biyu sun kece raini a wata babbar kasuwa da ke kan titin Ahmadu Bello Way a garin Jos, babban birnin jihar Plateau, a ranar Litinin.
Ko da yake har yanzu ba a bayyana dalilin fadan ba, wani mai amfani da kafafen sada zumunta ya ce matsalar ta taso bayan wani dan sanda ya hana wani jami’in soja kama wani dan kasuwa.
Bello Lukman, mai amfani da kafafen sada zumunta, ya wallafa wani rubutu game da lamarin a shafin sa na Facebook: “An yi wa wani dan sanda duka kuma aka kwace masa bindiga a jiya a cibiyar GSM da ke yankin Hamaz na Jos, babban birnin jihar Plateau.
Sojan ya fusata saboda dillalin wani mai gyaran waya ya lalata masa waya maimakon ya gyara. Ya so ya kama shi amma dan sandan ya hana sojan yin hakan.” ’Yan sandan sun ce a maimakon haka ya kai shi ofishin ‘yan sanda. Sojan ya kira wasu abokan aikinsa waɗanda suka zo wurin a cikin wata Hilux. Sun yi wa ‘yan sandan duka, sun raunata shi, suka tafi da bindigarsa.
Mai magana da yawun Rundunar yan’sanda na jihar SP Alabo Alfred, ya bayyana cewa an shawo kan lamarin kuma ya yi kira ga mazaunan yankin da su ci gaba da ayyukansu na yau da kullum ba tare da tsoro ba.









