Home Labarai Shugaban Majalisar Dokokin Kano Ya Taya Premier Radio Murnar Cika Shekaru Huɗu

Shugaban Majalisar Dokokin Kano Ya Taya Premier Radio Murnar Cika Shekaru Huɗu

82
0

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya taya gidan rediyon Premier Radio murnar cika shekaru huɗu da fara gabatar da shirye-shirye.

Shugaban yane Majalisar ta amince da bukatar da gaggawa.

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Gaya

Barau ya yaba wa Shugaban Ƙasa kan daƙile yunƙurin juyin mulki a ƙasar Benin

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar, inda ya bayyana cewa Falgore ya yabawa Premier Radio bisa jajircewarta, hangen nesa da kuma ƙudurin gabatar da shirye-shirye masu tasiri a matakin ƙasa da ƙasa.

Sanarwar ta ce nasarorin da gidan rediyon ya samu cikin shekaru huɗun sun nuna ƙwazo, aiki tare da jajircewa wajen isar da sahihan labarai da shirye-shiryen ilmantarwa ga al’ummar Jihar Kano da ma masu sauraro a ƙasashen waje.

Shugaban Majalisar ya kuma tabbatar da ƙudurin Majalisar Dokokin Jihar Kano na ci gaba da haɗin gwiwa da Premier Radio domin wayar da kan al’umma game da ayyukan majalisa da nauyin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya dora mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 2   +   10   =