Home Afrika Barau ya yaba wa Shugaban Ƙasa kan daƙile yunƙurin juyin mulki a...

Barau ya yaba wa Shugaban Ƙasa kan daƙile yunƙurin juyin mulki a ƙasar Benin

235
0

Mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma mataimakin kakakin majalisar ECOWAS na Farko, Sanata Barau Jibrin, ya yaba wa shugaba Bola Tinubu, saboda kai dauki gaggawa da ya yi ga bukatar gwamnatin Jamhuriyar Benin na neman taimakon sojojin Najeriya domin dakile yunƙurin juyin mulki a ƙasar.

A ranar Lahadi, wasu sojoji sun bayyana hambarar da Shugaba Patrice Talon ta hanyar wani jawabi da suka yi a gidan talabijin na kasar.

Sanata Barau, cikin wani bayani da Mataimakinsa na Musamman kan Yaɗa Labarai da Jama’a, Ismail Mudashir, ya fitar, ya yi godiya ga Shugaba Tinubu bisa saurin da ya nuna wajen amsa bukatar ƙasar.

Ya bayyana cewa saurin shiga tsakani na rundunar sojin Najeriya ya taka muhimmiyar rawa wajen tarwatsa juyin mulkin da dawo da doka da oda a ƙasar Benin.

Yayin da yake bayyana dimokuraɗiyya a matsayin ingantacciyar hanyar mulki, Sanata Barau ya ce mulkin soja bai da gurbi a tsarin duniya na zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   3   =