Home Labarai Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha a...

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Gaya

190
0

Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar kafa Kwalejin kimiyya da fasaha wato Polytechnic, a karamar hukumar Gaya, domin bawa bangaren zartarwa damar samar da Kwalejin kamar yadda gwamnan Alhaji Abba Kabir Yusif ya bukata tunda farko.

Da yake karin bayanin akan dokar, Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Dala, ya ce maƙasudin samar da Kwalejin shi ne don sauƙaƙawa ɗaliban da ke son koyon harkokin kimiyya daga kudancin Kano da bunkasa fannin ilimi.

Haka zalika a zaman majalisar, kwamiitin da aka dorawa alhakin bincikar badakalar da ake zargin dakataccen shugaban karamar hukumar Rano da aikatawa, ya bukaci a kara masa mako daya domin ya gabatarwa da zauren rahoton binciken da yayi,

Ya kuma bukaci a kyale mataimakin shugaban karamar hukumar ya ci gaba da rikon karamar hukumar har kwamitin ya bada rahoton sa.

Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewar, Majalisar ta dakatar da shugaban karamar hukumar ta Rano ne daga mukamin sa sakamakon korafi da aka yi akan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   8   =