Home Wasanni Shin Nigeria zata iya wuce wannan mataki a gasar kafi ta AFCON?

Shin Nigeria zata iya wuce wannan mataki a gasar kafi ta AFCON?

122
0

A yau Litinin ne Najeriya za ta ɓarje gumi da Mozambique a wasan zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta cin kofin Afirka da ake gudanarwa a Morocco.

Morocco Ta Yi Nasara a Wasan Bude Gasar AFCON 2025

Fitattun ƴan ƙwallon Najeriya da ba za su buga gasar Afcon ta 2025 ba

AFCON 2025: Najeriya Ta Fitar da Sunayen ‘Ƴan Wasanta 28

Za a fara karawa tsakanin Masar da Benin da karfe biyar na yammaci daidai da agogon Najeriya da Niger, sai a kece raini tsakanin Najeriya da Mozambique da karfe takwas na dare daidai da agogon Najeriya da Niger.

Super Eagles ta yi ta ɗaya a rukuni na uku da maki tara, ita kuwa Mozambique tana daga cikin huɗun da aka yi wa alfarmar zuwa zagaye na biyun da maki uku daga rukuni na shida da ta yi ta uku.

Masar ma ita ce ta yi ta ɗaya a rukuni na biyu da maki bakwai, Benin kuwa alfarma aka yi mata daga rukuni na huɗu da maki uku, bayan karewa a mataki na uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 1   +   6   =