Jam’iyyun adawa na (ADC) da LP sun soki Shugaban Bola Ahmed Tinubu bisa tafiyarsa zuwa Turai domin hutun ƙarshen shekara, daidai lokacin da ƙasar nan ke fuskantar ƙalubalen tsaro, ciki har da batun tsoma bakin sojojin Amurka a Arewa.
Jam’iyyar ADC ta zargi EFCC da amfani da siyasa wajen kin bada belin tsohon Ministan Shari’a
INEC za ta gana bangarorin dake rikici a jam’iyyar ta PDP
Gwamna Agbu Kefas Zai koma Jam’iyyar APC – Shugaban Jam’iyyar Taraba
Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar a ranar Lahadi cewa Tinubu ya bar Lagos zuwa Turai domin hutun ƙarshen shekara, gabanin wata ziyarar aiki da zai kai Abu Dhabi a Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ake sa ran zai halarci taron Abu Dhabi Sustainability Week Summit na shekarar 2026.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa an gayyaci Tinubu ne ta hannun Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, domin halartar taron da ke haɗa shugabanni, yan kasuwa da ƙungiyoyin farar hula don tattauna hanyoyin bunƙasa cigaba mai ɗorewa.
Sai dai, jam’iyyar ADC, ta bakin Sakataren Yaɗa Labaranta na Ƙasa, Bola Abdullahi, ta ce lokacin tafiyar bai dace ba duba da halin tsaron da ƙasar ke ciki. Jam’iyyar ta ambaci fashewar bam da ta yi sanadin mutuwar mutane a Zamfara, da kuma rahotannin shigowar sojojin Amurka Najeriya, tana mai cewa matakin Shugaban Ƙasa ya nuna rashin kulawa.









