Home Afrika Jam’iyyar ADC ta zargi EFCC da amfani da siyasa wajen kin bada...

Jam’iyyar ADC ta zargi EFCC da amfani da siyasa wajen kin bada belin tsohon Ministan Shari’a

106
0

Jam’iyyar ADC ta zargi Hukumar EFCC da amfani da siyasa wajen kin bada belin tsohon Ministan Shari’a na kasa, Abubakar Malami SAN.

Jam’iyyar ta ce babu wata shaida da ke nuna cewa Abubakar Malami ya karya sharuɗan belin da aka ba shi.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, jami’iyyar ADC ta ce an ɗauki matakin ne jim kaɗan bayan Abubakar Malami ya halarci wani taron siyasa a Jihar Kebbi.

ADC ta ce tana goyon bayan yaƙi da cin hanci da rashawa tare da mara wa EFCC baya wajen gudanar da aikinta.

Sai dai jam’iyyar ta yi gargaɗin cewa ɗaukar matakai na ɓangare ɗaya kan ‘yan adawa, na iya rage amincewar jama’a da kuma raunana sahihancin yaƙi da cin hanci a ƙasar.

Jam’iyyar ta kuma ce babu wata hukuma ta gwamnati da ke da ikon hana ɗan ƙasa shiga harkokin siyasa ba tare da umarnin kotu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 9   +   3   =