Kotun hukuntan manyan laifuka ta Bangladesh ta zartas da hukuncin kisa kan tsohuwar Firaministar ƙasar Sheikh Hasina bayan samunta da laifin keta haƙƙin ɗan adam sakamakon umarnin da ta bayar na buɗe wuta kan ɗaliban da ke zanga-zanga a bara, lamarin da ya kai ga hamɓarar da ita daga kujerar mulkinta.
Hukuncin kotun na yau Litinin ya buƙaci mahukuntan India su taso ƙeyar Sheikh Hasina mai shekaru 78 zuwa gida don a aiwatar mata da hukuncin na kisa, bayan da ta yi umarnin kisan ɗaliban da yawansu ya kai dubu 1 da 400 a zanga-zangar da suka gudanar da ƙalubalantar salon kamun ludayinta.
Baya ga hukuncin kisa ga Hassina Kotun ta kuma buƙaci gwamnatin riƙon ƙwaryar Bangladesh ta biya diyyar ilahirin mutanen da aka kashe yayin zanga-zangar dama waɗanda suka jikkata, wanda kuma tuni gwamnatin ta yi maraba da shi tare da bayyana hukuncin a matsayin mai cike da tarihi, yayinda ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankulansu.
An faro wannan shari’ar ne ba tare da zuwan Hasina gaban kotu ba, kasancewar tana samun mafaka a India tun bayan hamɓarar da ita a 2024, sai dai tuni ta yi tir da wannan hukunci yayinda ma’aikatar harkokin wajen India ta bayyana hukuncin a matsayin rashin adalci.
Jim kaɗan bayan sanar da wannan hukunci da kotun ta yi ne, dubban matasa suka sake bazama tituna yayinda wasu suka fara aikin rushe gidan iyayen Hasina wanda aka mayar gidan tari sakamakon gagarumar gudunmawarsa ga kafuwar ƙasar ta Bangladesh, kodayake tuni mahukunta suka ɗauki matakin dakatar da su.
Babu dai tabbacin ko India za ta miƙa Hassina ga Bangladesh don fuskantar hukunci, lura da yadda alaƙar ƙasashen biyu ke tangal-tangal, kuma Indiyar ke kallon hukuncin a matsayin rashin adalci.
Har kawo yanzu dandazon matasa ne ke ci gaba da zanga-zanga a tsakar biranen Bangladesh tare da ƙona tayoyi.









