Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya buƙaci jam’iyyar PDP da ta ɗage babban taronta da ta shirya yi tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan nan na Nuwamba, a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Ya ce ci gaba da shirin gudanar da taron duk da irin wasiƙun dakatarwa da kotuna suka bayar zai ƙara ta’azzara rikicin jam’iyyar sannan ya jefa ta cikin matsaloli a nan gaba.
Bukola Saraki ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan karɓar baƙuncin ƴan kwamitin amintattun jam’iyyar ƙarƙashin shugabancin Ambasada Hassan Adamu, a gidansa.
Tawagar dai ta ziyarci Bukolan ne domin neman tabarrukinsa da shawarwari kan yadda za a cimma haɗin kai a jam’iyyar da ta samu rarrabuwar kai.









