Home Labarai Bai kamata WIke da AM Yerima su yi sa-in-sa a bainar jama’a...

Bai kamata WIke da AM Yerima su yi sa-in-sa a bainar jama’a ba – Matawalle

105
0

Ƙaramin ministan tsaro na Najeriya, Bello Matawalle ya ce babu buƙatar yin sa-in-sar da aka samu tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da sojan ruwa, AM Yerima.

A wata hira da kafar DCL, Matawalle ya ce ya kamata a magance matsalar da ta haifar da cece-kucen ta hanyar tattaunawa maimakon yin sa-insa a bainar jama’a.

Mr Wike dai ya umarci sojoji da ke gadin wani fili su kauce domin bari shi da jami’ansa su shiga filin, amma jami’an sojin a ƙarƙashin jagorancin wani matashin hafsan sojin ruwa suka jajirce cewa umarni aka ba su kuma ba za su bari a yi akasin umarnin da suke aiki a kai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   2   =