Home Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Janye Shirin Karɓar Harajin 15% Kan Man Fetur da...

Gwamnatin Tarayya Ta Janye Shirin Karɓar Harajin 15% Kan Man Fetur da Dizel

260
0

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da shirin karɓar harajin kashi 15 cikin 100 da ta shirya fara karɓa kan man fetur da dizel da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa, Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), ce ta sanar da hakan cikin wata takardar da mai magana da yawunta, George Ene-Ita, ya fitar a ranar Alhamis.

AU Ta Musanta Zargin Trump Kan Kisan Kiristoci a Najeriya

Bai kamata WIke da AM Yerima su yi sa-in-sa a bainar jama’a ba – Matawalle

A cewar sanarwar, dakatarwar ta biyo bayan nazari da kuma tattaunawa da hukumomi da kamfanonin da abin ya shafa, domin kauce wa tasirin da hakan zai iya yi kan farashin man fetur a ƙasar.

A ranar 29 ga watan Oktoba ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da saka wannan haraji, wanda a cewar gwamnati, manufarsa ita ce ƙarfafa matatun mai na cikin gida da rage dogaro da shigo da man waje.

Sai dai gwamnati ta shirya fara aiwatar da harajin daga ranar 21 ga watan Nuwamba, kafin hukumar NMDPRA ta janye matakin, bisa la’akari da yanayin tattalin arziki da halin da ‘yan ƙasa ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   7   =