Ƙaramin Ministan Harkokin Tsaro, Bello Matawalle, ya soki yadda Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya gudanar da sa-in-sa da jami’in soja a wani fili da ake takaddama a Abuja.
Matawalle ya ce Wike bai saurari shawarar Babban Hafsan Tsaro (CDS) da Shugaban Rundunar Sojin Ruwa (CNS) ba kafin ya tafi wurin, duk da cewa an shawarce shi a bar rundunar ta bi hanyoyin da suka dace wajen warware matsalar.
A wata hira da DCL Hausa a ranar Laraba, ministan tsaro ya bayyana abin da ya faru a matsayin “abin takaici,” yana mai cewa jami’in da abin ya shafa yana aiki ne bisa doka kuma yana bin ƙa’idojin soja.
“Abin da ya faru tsakanin Minista Wike da jami’in soja abin takaici ne. Lokacin da Wike ya isa wurin, jami’in ya bayyana masa cewa shi kawai umarni ya ke bi,” in ji Matawalle.
Ministan ya ƙara da cewa: Wike bai kamata ya yi musayar yawu da jami’in ba; ya kamata ya kai korafinsa ta hanyar manyan jami’an soja da ke sama da shi.”









