Home Labarai AU Ta Musanta Zargin Trump Kan Kisan Kiristoci a Najeriya

AU Ta Musanta Zargin Trump Kan Kisan Kiristoci a Najeriya

110
0

Shugaban hukumar gudanarwar AU, Moussa Faki Mahamat, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin New York a ranar Laraba.

A cewarsa, irin wannan magana na iya tayar da tarzoma da rikici idan ba a yi taka-tsantsan ba, musamman a yankin da ke fama da kalubalen tsaro.

Faki ya ce, “Bincikenmu ya nuna cewa mafi yawan mutanen da rikicin ya ritsa da su a arewacin Najeriya, Musulmai ne, ba Kiristoci ba,” yana mai cewa akwai hujjoji masu karfi da ke tabbatar da hakan.

Tun daga shekarar 2009, rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40,000 tare da tilasta wa sama da miliyan biyu barin gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya(UN).

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta karyata ikirarin da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi cewa ana kai wa Kiristoci hare-haren kisan kiyashi a yankin arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   2   =