Gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta yi ƙarin haske kan rahotonnin da ke cewa tana shirin sakin wasu da ake zargi da kasancewa ƴan fashin daji da hukumomin suka kama a baya.
‘Yanbindigar Da ke Addabar Kano Daga Jihar Katsina Suke – Gwamnan Kano
Yan’bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Zamfara
’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 a Jihar Filato
Rahotonnin wasu kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa gwamnatin jihar na shirin sakin wasu ƴan fashin daji kimanin 70 da ake tsare da su, bayan kama su da zargin fashin daji da garkuwa da mutane.
Sai dai kwamishinan al’amuran tsaro da cikin gida na jihar, Hon. Nasiru Mu’azu ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu ba a kammala tantance adadin mutane da gwamnatin ke shirin saki ba.
Ya ce gwamnatin ta ɗauki matakin sakin mutanen ne kasancewa yana cikin sharuɗɗan yarjejeiniyar zaman lafiya da wasu al’umomin jihar suka cimma da ƴanbindigar a garuruwansu









