Yan bindiga sun kashe wani jigon jam’iyyar APC a Zamfara mai suna Umar Moriki a ranar 15 ga Nuwamba, 2025.
An harbe Moriki ne kusa da kauyen Fegi, a cikin karamar hukumar Tsafe kan hanyar Gusau zuwa Tsafe, a jihar Zamfara.
An kashe shi ne da sanyin safiyar ranar Asabar, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Gusau.
Kafin rasuwarsa, Moriki ya halarci wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC wanda Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya shirya.
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar tasa, inda ta bayyana ta a matsayin babban rashi ga jam’iyyar da ma jihar.
Moriki, mai shekaru 62, ya taba rike mukamin mataimakin shugaban karamar hukumar Zurmi, kuma ya rike wasu mukamai da dama a fannin siyasa. Ya kuma yi takarar kujerar dan majalisar tarayya ta Zurmi/Shinkafi a zaben 2023.
Wannan lamari dai wani bangare ne na ci gaba da matsalar rashin tsaro da ‘yan fashi da garkuwa da mutane ke yi a jihar Zamfara.









