Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaro a fadar sa da ke Abuja.
Amurka ta Jinjinawa Najeriya kan ceton Dalibai 100 na St. Mary’s
Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta fara ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Litinin.
Wannan ita ce ganawa ta farko da Shugaban Ƙasar ya yi da hafsoshin tsaron tun bayan rantsar da sabon Ministan Tsaro, Christopher Musa, a ranar 4 ga watan Disamba da muke ciki.
Ko da yake ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna ba, ana hasashen ganawar ta mayar da hankali ne kan ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar, musamman matsalar garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.








