Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta musanta rahotannin da ke yawo cewa jirginta kirar C-130 da ya yi saukar gaggawa a birnin Bobo-Dioulasso na ƙasar Burkina Faso, yana gudanar da aikin leken asiri a ɓoye.
Rundunar ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya marar tushe, tana mai jaddada cewa jirgin na kan hanyarsa zuwa ƙasar Portugal ne domin a yi masa gyara. Ta ce saukar gaggawar da jirgin ya yi ya biyo bayan matsalar tsaro, kamar yadda dokokin sufurin jiragen sama na duniya suka tanada.
A cewar bayanan da jaridar The Nation ta rawaito, wata majiya a hedkwatar tsaron NAF ta tabbatar da cewa jirgin na ɗauke da dukkan takardun izini da suka dace, kuma an bi duka ƙa’idoji da matakan doka da suka shafi tafiye-tafiyen jiragen sama na soja.









