A ranar Litinin ne gwamnatin Jamhuriyar Benin da ke Yammacin Afirka ta sanar da rufe ofishin jakadancinta da ke Yamai na Jamhuriyar Nijar, a wani abu da masana ke bayyanawa da taɓarɓarewar alaƙa tsakanin ƙasasashen biyu.
Barau ya yaba wa Shugaban Ƙasa kan daƙile yunƙurin juyin mulki a ƙasar Benin
Gwamnatin tarayya za ta fara sabbin dokokin haraji daga 1 ga wata janairu,2026.
A cewar hukumomin ƙasar ta Benin, sun ɗauki matakin ne bayan wasu lamurra da suka fi ƙarfinsu, kodayake ba ta fitar da wani ƙarin bayani a hukumance kan lamarin ba.
A nata ɓangare ita ma Jamhuriyar Nijar ta mayar da martani kan wannan mataki, in da ta umarci jami’in diflomasiyyar Benin ya saka hannu kan takardar dakatar da aiki, sannan ya bar ƙasar cikin sa’o’i 48.
Lamarin ya faro ne tun bayan da hukumomin Benin suka ɗauki matakin korar shugaban hukumar leƙen asirin Nijar da ke birnin Cotonou da kwamishiniyar ƴansanda da ke ofishin jakadancin Nijar a Cotonou bisa zargin aikata zagon ƙasa.
Inda a ranar 1 ga watan Janairu ma’aikatar harkokin wajen Nijar ta ayyana Seidou Imourana, babban jami’in diplomasiyyar ofishin jakadancin Benin a matsayin wanda ba a buƙatar zamansa a ƙasar, tare da umartarsa da ficewa daga ƙasar.









