Home Labarai Gwamnatin Kano Ta Biya Naira Biliyan 2 Don Karɓo Takardun Daliban Lafiya...

Gwamnatin Kano Ta Biya Naira Biliyan 2 Don Karɓo Takardun Daliban Lafiya a Cyprus

205
0

Gwamnatin Kano ta ce ta biya kimanin naira biliyan 2 domin karbo takardar shaidar kammala karatun daliban da gwamnatocin baya suka tura yin karatun lafiya a kasar Cyprus.

Alamu Sun Nuna Yiwuwar Ficewar Gwamna Abba Kabir Daga NNPP Zuwa APC

Samarin Tijjaniyya sun gudanar da taron zaman lafiya a Kano

Kotun Tarayya Ta Umarci EFCC Ta Gurfanar da Kwamishinan Kuɗi na jihar Bauchi Kan Zargin Safarar Naira Biliyan 4.6

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan, lokacin da yake bada shaidar karatun ga dalibai 10 daga cikin wadanda aka tura karatun kuma sai yanzu sakamakon su ya iso Kano.

A cewar gwamna Abba abin takaici ne yadda gwamnatin data gabata tayi biris da lamuran daliban duk kuwa da irin alfanun da zasu yiwa al’ummar Kano, gwamnan ya kuma yiwa matasan 10 albishirin basu aikin gwamnati da zarar sun gama bautar kasa.

Gwamna Yusif ya kuma roki matasan dasu girmama wahalar da iyayen su da gwamnati suka yi dasu ta hanyar zaunawa a Kano domin tallafawa al’umma ba tare da sun gudu wata kasar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 0   +   4   =