Rikicin manoma da makiyaya ya sake kunnu tare da sanadiyar mutuwar mutum guda, da kuma asarar dukiya.
An Kama Ni Ne Saboda Binciken Badakalar Ganduje A Dala Dry Port – Muhuyi
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta mayar da sama da naira miliyan 50 ga mahajjatan
Rikicin ya faru ne a unguwar Yalwa dake Karamar Hukumar Guri a jihar, a daren Asabar wayewar garin Lahadi.
Malam Ado Musa, wani manomi daga yankin, ya zargin makiyaya dauke da makamai da kai farmaki kauyen a inda suka ƙone gidaje da injinan nika shinkafa na gargajiya.
Jami’an tsaro sun isa wajan domin shawo kan rikicin da kuma shiga tsakanin manoman da kuma makiyaya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan sabon rikici ya samo asali ne daga tashin hankali da ya dade yana faruwa, tun bayan kashe wani manomi mai suna Ya’u Namara a shekarar data gabata.
Sabon rikicin ya zo ne ‘yan kwanaki bayan wani makamancin rikici a kauyen Zarga dake yankin ƙaramar hukumar Taura, inda aka jikkata manoma guda 12.








