Home Labarai Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta mayar da...

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta mayar da sama da naira miliyan 50 ga mahajjatan

98
0

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta mayar da sama da naira miliyan 50 ga mahajjatan jihar da ke shirin sauke farali a shekarar 2026, sakamakon rage kudin Hajj da Hukumar Kula da Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar.

Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, an mayar da kudaden ne ga mutanen da suka riga suka biya kafin a sanar da sabon tsarin rage kudin tafiya.

Ahmed Labbo ya bayyana cewa NAHCON ta sabunta kudin Hajj na shiyyar Arewa, inda farashin yanzu ya kai sama da naira miliyan 7.6.

Ya kara da cewa umarnin mayar da kudaden ya fito ne daga hukumar, sakamakon raguwar guraben mahajjata da aka samu na badi.

Ya yabawa jami’an hukumar na sassa daban-daban bisa kokarin da suka yi wurin tattara bayanan masu neman zuwa aikin Hajj.

Game da shirin gudanar da aikin Hajjin 2026, Labbo ya ce hukumar na ci gaba da kokarin samar da mafi kyawun tsari domin jin dadin alhazan Jigawa a Ƙasar Saudiyya.

Ya kuma yi kira ga dukkan masu niyyar zuwa Hajj da su tabbatar sun kammala biyan kuɗin kujerunsu kafin ranar 24 ga Disamba, 2025.

Daraktan ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da gudanar da aikin Hajj na 2026 ba tare da wata tangarda ba.

Haka kuma ya mika godiya ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa goyon bayan da yake baiwa hukumar a kai a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 1   +   2   =