Home Ketare Paris: Tsohon Jagoran ’Yan Tawayen Congo Ya Samu Daurin Shekaru 30

Paris: Tsohon Jagoran ’Yan Tawayen Congo Ya Samu Daurin Shekaru 30

25
0

wata kotu a birnin Paris, ta yankewa tsohon madugun ’yan tawayen Congo, Roger Lumbala, hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari, bayan samun sa da laifin aikata munanan laifukan cin zarafin bil’adama a gabashin ƙasar shekaru kusan 20 da suka gabata.

Najeriya ta ƙaryata zargin leken asiri kan jirgin sojinta a Burkina Faso ‎

ECOWAS zata buɗe babban taron ƙoli a yau Lahadi.

Burkina Faso Har Yanzu Ba Ta Saki Jirgin Yaƙin C-130 da Sojojin Najeriya 11 Ba

Kotun ta same shi da laifin azabtarwa da kuma fyade a lokacin Yaƙin Congo na Biyu.

Roger Lumbala, wanda ya nemi mafaka a Faransa, an kama shi ne maimakon ba shi kariya.

Lauyan da ke kare shi ya bayyana cewa laifukan da ake zargin an aikata su ne shekaru da dama da suka wuce, kuma ba a ƙasar Faransa aka yi su ba.

Sai dai kotun ta ƙi amincewa da wannan hujja.

A halin yanzu, Lumbala na da kwanaki goma na ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 2   +   6   =