Home Labarai NLC Ta Shirya Zanga-Zanga a Ranar 17 Ga Disamba

NLC Ta Shirya Zanga-Zanga a Ranar 17 Ga Disamba

96
0

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta sanar da gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya a ranar 17 ga watan Disamba, sakamakon yadda matsalar tsaro ke ta’azzara a sassa daban-daban na kasar.

Kotun Bangladesh ta yanke tsohuwar Firaminista Hasina hukuncin kisa

Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya ta kama Alwan Hassan

 

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana haka cikin wata sanarwa bayan taron masu ruwa da tsaki na kungiyar da aka gudanar a daren Litinin a Lagos.

Kungiyar ta nuna damuwa kan harin ’yan bindiga da ya yi sanadin sace dalibai mata 24 a Jihar Kebbi, lamarin da ta ce ya faru ne bayan an janye jami’an tsaro da ke gadin makarantar.

A cewar NLC, yawaitar hare-haren garkuwa da dalibai a kwanakin nan abin tashin hankali ne, wanda ya zama dole gwamnati ta dauki matakai na gaggawa domin dakile matsalar tsaro a fadin kasa.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro su kara ba fannin tsaro muhimmanci, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   2   =