Home Labarai Matawalle ne ya sanya Badaru Ajiye Mukaminsa na Babban Ministan Tsaro

Matawalle ne ya sanya Badaru Ajiye Mukaminsa na Babban Ministan Tsaro

117
0

 

Tsohon Babban Ministan Tsaro na ƙasa, Mohammed Badaru Abubakar, ya mika takardar murabus daga mukaminsa a ranar 1 ga Disamba 2025, inda ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda “lalura ta rashin lafiya wacce yake fatan cigaba da neman magani.” Wannan sanarwa ta fito daga ofishin fadar Shugaban Kasa, ta bakin kakakinsa kan yada labarai, Bayo Onanuga.

Haka zalika, bayan karɓar murabus ɗin, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Tsohon Janar Christopher Musa a matsayin sabon Babban Ministan Tsaro na ƙasa.

Amma duk da dalilin murabus ɗin da ya bayyana na rashin lafiya, wasu rahotanni daga jaridun cikin gida sun ƙaryata hakan, suna danganta ajiye mukamin Badaru da zargin sabani mai tsanani da Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle. Wata majiya daga cikin ma’aikatar tsaro ta bayyana cewa rikicin ya shafi yadda ake tafiyar da ma’aikata da rarraba aiki, wanda ya jawo rashin aiki yadda ya kamata a wasu sassa.

Duk da cewa wannan zargin ya yi yawo, ba a sami wata sanarwa ta hukuma da ta tabbatar da shi ba. Badaru da kansa ya musanta wasu rahotanni da ke cewa saukar tasa ta samo asali ne daga wasu dalilai siyasa ko tsare-tsaren ƙasashen waje.

A halin yanzu, jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro suna cigaba da sa ido kan yadda sabon minista zai gudanar da ayyuka, musamman a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsalolin tsaro da dama.

Biyo bayan murabus ɗin Badaru, jama’a da dama suna neman ƙarin bayani kan asalin dalilan da suka sa ya sauka don tabbatar da gaskiyar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 1   +   5   =