Home Labarai Jam’iyar ta rabu kashi biyu, kuma kundin shari’a ya ba su izinin...

Jam’iyar ta rabu kashi biyu, kuma kundin shari’a ya ba su izinin barin jam’iyar

150
0

‘Yan majalisar Rivers ba su sanar da ni kafin ficewar su daga jam’iyyar PDP Nyesom Wike, Babban Ministan Tarayya, ya ce ‘yan majalisar wakilai na jihar Rivers waɗanda suka bar Jam’iyyar PDP zuwa APC ba su sanar da shi kafin su yanke shawarar ba.

A ranar Juma’a, ‘yan majalisa 17 na jihar Rivers,ciki har da Martin Amaewhule, shugaban majalisar, suka bar Jam’iyyar PDP domin komawa jam’iyyar APC. Kwanaki Biyu kkafin barin su daga jam’iyyar, majalisar wakilai ta Rivers ta amince da shugaban ƙasar Bola Tinubu, suna bukatar da ya ƙara tsayawa takara.

A cikin jawabi da ya bayar a Abuja a ranar Juma’a, yayin zagayen duba ayyukan gadar da ake ginawa, Wike ya ce ‘yan majalisar suna da ‘yanci su shiga kowace jam’iya da suka zaɓa. Ya ce abin ya zo saboda rikicin da ke cikin PDP, kuma zai ci gaba da aiki da sauran membobin jam’iyar. Jam’iyar ta rabu kashi biyu, kuma kundin shari’a ya ba su izinin barin jam’iyar,” in ji Wike.

Wannan abin ya faru ne sanadiyyar rikicin siyasa da ke faruwa a Rivers tun da tenuwar Wike ta kare a matsayin gwamna sannan ya aka bashi mukamin Minista, har takai da sunyi rigima da gwamnan jihar Siminalayi Fubara.

‘Yan majalisar 16 ko 17 (a cewar wasu rahoto) sun shiga APC don “haɗin kai da shugaban ƙasa,” saboda sun ga cewa PDP ta rabu kashi biyu. Wike ya ce zai ci gaba da goyon bayan PDP, amma ya ce jam’iyar dole ta gyara domin dawo da ita yanda take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 5   +   6   =