Home Labarai Kotu ta umarci ma’aikatan birnin tarayya su dakatar da yajin aiki

Kotu ta umarci ma’aikatan birnin tarayya su dakatar da yajin aiki

45
0

Kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago ƙarƙashin jagorancin Alƙali Emmanuel Subilim ta umarci ma’aikatan babban birnin tarayya FCTA da su dakatar da yajin aikin da suke yi har sai kotu ta saurari ƙarar da aka shigar.

Gwamnan Kano zai koma jam’iyyar APC ranar Litinin

Sojojin da suka taɓa kitsa juyin mulki a Najeriya da abin da ya faru da su

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai jagoranci shari’a kan kisan matar aure da ‘ya’yanta shida a Dorayi

Wannan hukunci ya biyo bayan buƙatar ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, wanda ya nemi kotu ta tilasta wa ma’aikatan da ke yajin aikin su koma ayyukansu.

A cikin karar, Wike ya sanya shugaba da sakataran haɗakar ƙungiyar ƴan ƙwadago JUAC a matsayin waɗanda ake kara.

Alƙalin ya ce dole ne a dakatar da duk wani yajin aiki idan har an shigar da kara a gaban kotun warware mtatsalolin ƴan ƙwadago domin a warware matsalar yadda ya kamata.

Ya kuma gargadi cewa rashin bin wannan doka na iya jawo hukunci ko ladabi.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga Maris, 2026.

Ma’aikatan dai sun shiga yajin aikin ne tun daga ranar 19 ga watan Janairu inda suka buƙaci gwamnatin tarayya ta kyautata yanayin aikinsui da alawu-alawus din su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 8   +   8   =