Home Tsaro Yadda mayaƙa ke sabonta salon kai hari da jirage marasa matuƙa a...

Yadda mayaƙa ke sabonta salon kai hari da jirage marasa matuƙa a Najeriya da wasu ƙasashen

76
0

Ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi na ƙara yawan ahare-haren da suke kaiwa ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa a Najeriya da ƙasashen Yammacin Afirka.

 

Wannan na ƙara damuwar da ake da ita ta cewa mayaƙan na ƙara ƙarfi wajen samun damar kai hare-hare ta sama.

 

Wata cibiyar nazari kan matsalar tsaro mai suna Acled, ta ƙirga lokuta 69 da ƙungiyoyi masu alaƙa da al-Qaeda suka kai farmaki da jirage marasa matuƙa a ƙasar Burkin Faso da Mali tun daga shekarar 2023, yayin da ƙungiyoyi biyu masu alaƙa da ƙungiyar IS suka kai hari da jirage marasa matuƙa sau 20 – mafi yawansu a Najeriya, ƙasa da ta kwashe sama da shekara 20 tana fama da matsalar masu ɗauke da makami.

 

Harin jirgi maras matuƙi na baya-bayan nan da ƙungiyoyin suka kai shi ne wanda aka kai a jihar Borno ta arewa maso gabashin ƙasar ranar 29 ga watan Janairu.

Mayaƙan sun kai farmaki ta amfani da dakaru ta ƙasa, sai kuma suka yi amfani da da jirage marasa matuƙa a kan wani sansanin soji

Rundunar sojin Najeriya ta ce an kashe sojojinta tara a lokacin harin na ƙungiyar IS a yankin Yammacin Afirka, wato Iswap – wanda cibiyar nazari kan tsaro ta Acled ta bayyana a harin a amatsayin mafi girma ta fannin amfani da jirgi maras matuƙi a yankin.

 

Mayaƙan na amfani ne da ƙananan jirage marasa matuƙa marasa tsada wadanda ake iya samu a kasuwa, inda ake yi musu ɗamara da ababen fashewa.

 

Sannan kuma cibiyar ta ce mayaƙan na amfani da su wajen tattara bayanai da leƙen asiri lokacin shirye kai farmaki, kamar yadda babban mai sharhi kan tsaron Afirka na cibiyar Acled, Ladd Serwat ya bayyana wa BBC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   9   =