Home Labarai Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano Ta Amince da Mayar da Ragowar...

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano Ta Amince da Mayar da Ragowar Kuɗi ga Maniyatan Hajjin 2026

89
0

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince da biyan kuɗin da ya yi ragowa ga maniyatan aikin hajjin mutum ɗari da tara waɗanda suka fara ajiya kudin su daga naira million 8 da dubu 500,000 da kuma naira million 8 da dubu dari hudu da arba domin aikin Hajjin na shekarar 2026.

Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihar Kano, Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa.
Ya bayyana cewa, maniyatan aikin hajjin bana dari biyar da cansa’in da uku ne suka biya kuɗin ajiyar su tun kafin sanar da cikakken kuɗin Hajjin.

Lamin Rabi’u Danbappa ya yi kira ga sauran maniyatan aikin hajjin da abin ya shafa da su garzaya zuwa Hukumar domin karɓar kuɗinsu.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’ na hukumar jin dadin jihar Kano Suleman Abdullahi Dederi ya rawaito cewa, hukumar ta biya fiye da naira biliyan 23 ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa NAHCON a madadin waɗannan maniyyata da suka Biya kudadensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 10   +   3   =