Home Labarai Gwamnan Kano Ya Yaba wa Tinubu Kan Amincewa da Kammala Aikin Titi...

Gwamnan Kano Ya Yaba wa Tinubu Kan Amincewa da Kammala Aikin Titi na Wuju-Wuju Mai Naira Biliyan 47

95
0

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewar gwamnatin tarayya na kammala aikin titin Wuju-Wuju da kuɗin sa ya kai naira biliyan 47.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda gwamnan ya bayyana hakan yayin taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 35.

Gwamnan ya ce aikin titin an fara shi tun a shekarar 2013 a zamanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, amma ya tsaya cak tsawon shekaru takwas, lamarin da ya sa gwamnatin sa ta nemi sa hannun gwamnatin tarayya domin kammala shi.

Gwamna Yusuf ya kuma yaba da rawar da Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, ya taka wajen bibiyar aikin har aka amince da shi, inda ya bayyana shi a matsayin jakada nagari ga jihar Kano.

Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sanarwar na cewa gwamnan ya kuma roƙi Shugaba Tinubu da ya amince da ƙarin wasu manyan ayyukan a Kano, tare da tabbatarwa al’ummar jihar cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya domin samar da ci gaba mai ɗorewa

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 5   +   4   =