Dubban mutane sun rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a Mozambique
Dubban mutane ne suka rasa muhallansu sakamakon mummunan ambaliyar ruwa a Mozambique lamarin da ya tilasta wa Shugaban ƙasar, Daniel Chapo, soke tafiyarsa zuwa taron tattalin arziki na Duniya da za a gudanar a Davos a wannan makon.
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 18 daga hannun ‘yanbindiga a gaɓar tekun Kamaru
Ambaliyar ta lalata manyan gine-gine tare da shafar dubban mutane a sassa daban-daban na ƙasar yayin da Mozambique ke shiga lokacin damina na shekara-shekara.
Shugaban ya sanar da soke tafiyar ne a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce ƙasar “na cikin mawuyacin hali kuma mafi muhimmanci a wannan lokaci shi ne ceto rayuka.”
Aƙalla mutane 95 ne suka rasa rayukansu tun lokacin da ruwan sama mai ƙarfi ya fara tsakiyar Disamba adadin da hukumomi ke fargabar zai ƙaru yayin da ambaliyar ke ci gaba.
An samu ambaliyar ruwa a manyan larduna na Maput da, Gaza da Sofala, wanda ya shafi rayuwar dubban mutane
Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai (OCHA) ya ƙiyasta cewa fiye da mutum 400,000 abun ya shafa kuma ana sa ran wannan adadi zai ƙaru yayin da ruwan sama ke ci gaba.









