Home Afrika Musulmai ne suka fara fuskantar matsala ta hanyar hare-haren Boko Haram a...

Musulmai ne suka fara fuskantar matsala ta hanyar hare-haren Boko Haram a Nijeriya – AU

148
0

Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU), Mahmoud Youssouf, ya ce babu wani kisan kiyashi da aka yi wa Kiristoci a arewacin Najeriya, yana mai jaddada cewa Musulmai ne suka fara zama waɗanda Boko Haram ta fi kashewa tun farkon rikicin.

Da yake magana a Majalisar Dinkin Duniya a New York, Youssouf ya ce rikice-rikice a yankin ba su da sauƙin fassara, kuma ba za a kira su da kisan kiyashin Kiristoci ba.

Ya ce AU ta yi bayani a fili a sanarwarta cewa babu wani nau’i na kisan kiyashi ga Kiristoci a arewacin Najeriya.

A makonnin baya, wasu ’yan siyasa a Amurka sun yi zargin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya, lamarin da ya sa wasu ’yan majalisar Amurka su nemi a ɗauki matakin diflomasiyya kan gwamnati. Haka kuma, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya Najeriya cikin jerin “kasashen da ake cikin damuwa”.

Gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen, duk da cewa kungiyar CAN ta ce al’ummomin Kirista na fuskantar hare-hare akai-akai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 10   +   2   =