Home Labarai Amurka ta Jinjinawa Najeriya kan ceton Dalibai 100 na St. Mary’s

Amurka ta Jinjinawa Najeriya kan ceton Dalibai 100 na St. Mary’s

97
0

Gwamnatin Amurka ta yaba wa Najeriya kan nasarar ceto wasu daga cikin dalibai 100 na makarantar St. Mary’s da aka sace a Papiri, Jihar Neja, tana mai cewa hakan na nuna jajircewar gwamnati wajen magance matsalolin tsaro.

Amurka Za Ta Hana Biza Ga ‘Yan Najeriya Masu Hannu A Zargin Kisan Kiristoci

Ko sojojin Venezuela za su iya fito-na-fito da na Amurka?

Saudiyya da Qatar za su samar da Jirgin Ƙasa

Jami’in Amurka Riley Moore ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon godiya da ya wallafa a shafinsa na X, bayan ganawarsa da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, tare da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka da suka kawo ziyara Najeriya.

Moore ya ce tattaunawar ta kasance mai zurfi kuma cike da fahimtar juna, inda bangarorin biyu suka tattauna matakan da za su kara inganta tsaro a tsakanin kasashen.

Ya kuma bayyana kafa rundunar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka a matsayin wani muhimmin ci gaba, yana mai cewa hakan na nuni da shirye-shiryen gwamnati wajen aiki tare da Amurka domin fuskantar manyan matsalolin tsaro.

Sai dai ya kara da cewa duk da ci gaban da ake samu, akwai sauran muhimman matakai da ya kamata a dauka, amma abubuwa na ci gaba da tafiya a hanya madaidaiciya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   4   =