Zuwan katafaren jirgin ruwa na yaƙi mallakar Amurka mai suna Gerald R Ford, tekun da ke kusa da yankin Latin Amurka na ƙara fito da ƙaruwar zaman tankiyar da ke tsakanin Amurkar da ƙasar Venezuela.
Wannan ne lokacin da Amurka ta bayyana a yankin da ƙarfinta tun bayan 1989 lokacin da ta kutsa Panama.
Kamar yadda shekaru 30 da suka gabata aka zargi Manuel Norriego da safarar muggan ƙwaya, yanzu kuma ana zargin shugaban ƙasar ta Venezuela, Nicolas Maduro da irin zarge-zargen da iyalansa suka musanta.
Amurka ba ta fayyace matsayinta ba dangane da aikewa da jirgin yaƙin kusa da ruwan Venezuela.
A makon da ya gabata ne ministan tsaron ƙasar, Vladimir Padrino Lopez ya sanar da ɗaukar manyan matakan soji a ƙasa da ruwa da sama da kuma ƙarfin makamai masu linzami tare da amfani da sojojin sa kai na farar hula da ke faɗin ƙasar domin tare abin da gwamnatin Maduro ta bayyana da “barazana”.
A wani jawabi ta kafar talbijin, Pdrino Lopez ya ce Maduro bai wa rundunar soji kusan 200,000 umarnin zama cikin shiri.
Ana dai yi wa kasancewar jirgin ruwan yaƙin Amurka kallon wani ɗan ba na ɗaura ɗamarar yaƙi ga gungun masu safarar ƙwaya da ke gudanar da al’amuransu a Venezuela – ɗaya daga cikin hare-haren da Amurka ta ƙaddamar dai ya janyo rasa rayuka fiye da 80 da ke cikin jirgin kwale-kwale da jiragen ƙarƙashin ruwa.
Sai dai wasu masu fashin baƙi na yi wa matakin na Amurka kallon wani shirin kifar da gwamnatin Maduro wanda Amurka ke yi wa kallon ba halstacce ba tun bayan zaɓen bara da ƙasar ta yi da masu hamayya ke yi wa kallon mai cike da maguɗi.
Yaya ƙarfin sojin Venezuela yake?
Shin ko sojojin Maduro za su iya fafata wa da sojojin ƙasa mafi ƙarfin soji a duniya?
A watan Satumba, Maduro ya yi iƙrarin cewa mutum fiye da miliyan takwasu sun sanya hannu domin kare Venezuela sannan ya nuna yiwuwar bai wa ƙungiyoyin masu tayar da ƙyar baya miliyan takwas makamai.
Sai dai ƙwararru sun musanta alƙaluman.
“Ba gaskiya ba ne. Ƙididdigar ba ta kai haka ba. Maduron da bai ma iya samun ƙuri’a miliyan huɗu ba a zaɓen bara,” in James Story, tsohon jakadan Amurka a Bogota daga 2020 zuwa 2023, ya shaida wa BBC Mundo. ” Sannan kuma alƙaluman sojojin da ke barin aikin soja na da yawa.”
Wani rahoto da cibiyar nazarin dabaru ta ISS ta ƙiyasta cewa Venezuela na da sojoji 123,000 da kuma masu ɗauke da makamai 220,000 sai kuma sojoji 8,000 da ke jiran ko-ta-kwana.









