Home Siyasa Sojojin da suka taɓa kitsa juyin mulki a Najeriya da abin da...

Sojojin da suka taɓa kitsa juyin mulki a Najeriya da abin da ya faru da su

85
0

A ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026 ne rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da yunƙurin juyin mulki a ƙasar wanda aka yi a shekarar da ta gabata, inda ta ce ta samu wasu sojoji da zargin kitsa kifar da gwamnatin ƙasar.

Babu Tabbas Kan Ranar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Zai Koma Jam’iyyar APC

Gwamnatin Kano Ta Biya Naira Biliyan 2 Don Karɓo Takardun Daliban Lafiya a Cyprus

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano Ta Amince da Mayar da Ragowar Kuɗi ga Maniyatan Hajjin 2026

A cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce ta kammala bincikenta, inda ta samu wasu hafsoshin sojin ƙasar guda 16 da laifin yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Tinubu cikin watan Oktoban 2025.

A watan Oktoban da ya gabata ne dai rundunar tsaron ta sanar da kama sojojin tare da ƙaddamar da bincike a kan su, inda ta zarge su da rashin ladabi da saɓa wa dokokin aikin soji.

Sai dai a lokacin hukumomin tsaron ƙasar ba su tabbatar da yunƙurin na juyin mulki ba, amma ba da daɗewa ba sai gwamnatin ƙasar ta yi garambawul a ɓangaren, inda aka cire wasu manyan hafsoshi, sannan aka ƙara wa wasu matsayi.

Najeriya ta fuskanci juyin mulki a lokuta da yawa – tun bayan samun ƴancin kan ƙasar – a tsakanin shekarun 1966 zuwa 1993.

Sai dai tun bayan da ƙasar ta koma mukin dimokuraɗiyya a 1999, sai ya kasance ba a cika jin batun juyin mulki a ƙasar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 5   +   9   =