Home Siyasa 2027: Jonathan ya gana da Atiku a Abuja

2027: Jonathan ya gana da Atiku a Abuja

171
0

Muhawara ta barke a fagen siyasar kasar nan bayan wata ganawa da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya yi da tsohon shugaban kasa Good Luck Ebele Jonathan.

Abubakar Malami Ya Musanta Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci, Ya Ce Siyasa Ce Kawai

Jam’iyar ta rabu kashi biyu, kuma kundin shari’a ya ba su izinin barin jam’iyar

Faɗa ya kaure tsakanin jami’an soji da na ‘yansanda a garin jos jihar Filato.
Jiga-jigan ‘yan siyasan sun gana ne a ne a birnin tarayyar Abuja, inda Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasar Good Luck Jonathan har gida.

‘Yan siyasar biyu basu bayana abubuwan da suka tattauna ba, amma mutane da dama na alakanta ganawar ta su da shirye-shiryen tunkarar zaben shugaban kasa na 2027 mai zuwa.

Ana rade-radin cewa dukkansu, na sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2027 mai zuwa.

Atiku Abubakar na cikin wadanda suka jagoranci kifar da gwamnatin Good Luck Jonathan a zaben 2015 a a karkashin jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 10   +   6   =