Home Afrika WHO ta bayyana cewa An Samu Raguwar Kamuwa Da Cutar Tarin Fuka...

WHO ta bayyana cewa An Samu Raguwar Kamuwa Da Cutar Tarin Fuka A Najeriya

124
0
Tedros Adhanom Ghebreyesus, Director General of the World Health Organization (WHO) speaks during a bilateral meeting with Swiss Interior and Health Minister Alain Berset, not pictured, before signing a BioHub Initiative with a global Covid-19 Pathogen repository in Spiez laboratory on the sideline of the opening of the 74th World Health Assembly, WHA, at the WHO headquarters, in Geneva, Switzerland, Monday, May 24, 2021. (KEYSTONE POOL/Laurent Gillieron)

Binciken da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar a bana, ya nuna cewa akwai raguwar yawan mutanen da ke kamuwa da cutar tarin fuka (TB) a Najeriya, ciki har da jihar Kano.

Rahoton ya bayyana cewa sabbin matakan da hukumomi da abokan haɗin gwiwa ke ɗauka sun taka rawar gani wajen rage yaduwar cutar.

Shugaban Hukumar Dakile Yaduwar cututtuka ta jihar Kano Dakta Sulaiman Musa, ya bayyana cewa nasarar
“Nasarar da aka samu ba ta tabbata kai tsaye ba, sai da goyon bayan da gwamnatin Kano ke bayarwa ta fuskar kayan aiki da wayar da kan jama’a da kuma tallafawa cibiyoyin kula da masu fama da cututtukan.

“Da wannan ci gaba, har yanzu akwai bukatar ƙara azama wajen wayar da kan al’umma saboda da dama na cigaba da boye cutar ko kuma rashin kai kansu asibiti”. In ji shi.
‎Shugaban ya kuma yi kira ga al’umma da su rika zuwa asibiti idan sun fara ganin alamomin cutar TB kamar tari mai ɗorewa fiye da makonni biyu, rama ba tare da dalili ba, da kuma gajiya ko zufa da dare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 3   +   5   =