Home Labarai Sojojin Najeriya Sun Daƙile Harin Ƴanbindiga a Bitta, Borno, Sun Hallaka Wasu...

Sojojin Najeriya Sun Daƙile Harin Ƴanbindiga a Bitta, Borno, Sun Hallaka Wasu da Makamai da Kayayyaki da Aka Kwato

26
0

Wasu rahotanni na cewa sojoji sunyi nasarar daƙile yaƙunrin harin ƴanbindiga lokacin da suka nufi kai hari a cikin al’ummar Bitta da ke Borno.

Rundunar ce ta sanar da hakan a shafinta na X inda ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na tsakar daren jiya Alhamis lokacin da sojojin suka gano wannan yunƙuri na ‘yanbindiga da ke tafiya zuwa yankin.

A cewar rundunar, sai da sojojin suka bari ƴanbindigar suka shiga wani yanki da aka musu tarko kafin buɗe musu wuta, inda suka kashe wasu daga cikin maharan, ciki har da wani kwamandansu da mai ɗaukar musu hoto.

Rundunar ta ƙara da cewa, daga baya rundunar sojojin sama ta Operation Haɗin Kai ta kai farmaki kan waɗanda suka tsere lamarin da ya ƙara hallaka wasu tare da tarwatsa hanyoyin gudunsu.

A lokacin da ake fafatawa a yankin, an ruwaito cewa sojoji sun bi diddigin hanyoyi da dama, kuma sun gano kaburbura marasa zurfi, wanda ke nuna ƙarin asarar rayuka da aka yi wa ‘yan ta’addan a lokacin fafatawar.

Bayan fafatawar, sojoji sun gudanar da bincike a yankin inda suka ƙwato kayayyaki da makamai da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 5   +   1   =