Babban Jami’in tsaro na farin kaya Yayi Wa Tinubu Bayanin yadda Ake Kara Samun Karuwar Tsaro.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu bayanai daga Darakta Janar na Ma’aikatar Tsaron Jiha (DSS), Mista Tosin Adeola Ajayi, a daidai lokacin da ake samun karuwar matsalolin tsaro.
Sanarwar da Bayo Onanuga, Mai Ba da Shawara na Musamman ga Shugaban Kasa kan Labarai da Dabaru, ta ce an yi taron ne domin sanar da Shugaban Kasa halin da ake ciki a yanzu game da tsaro a kasar.
Kwanan nan, Najeriya ta fuskanci sabbin hare-haren rashin tsaro, ciki har da sace dalibai a jihohin Kebbi da Niger.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwanaki hudu bayan sace dalibai da dama daga makarantar sakandare da ke Maga, jihar Kebbi a ranar Litinin, ‘yan bindiga sun kai hari a harabar makarantar sakandiri ,Da wata makarantar Katolika da ke yankin Papiri a karamar hukumar Agwara ta jihar Neja, inda suka yi awon gaba da sama da dalibai 300 da ma’aikata 12.
Wannan ya haifar da rufe makarantu a wasu jihohi domin dakile barazanar tsaro.
A ranar Juma’a, Gwamnatin Tarayya ta sanar da rufe makarantun sakandare 41 na tarayya a yankunan da ke da hatsarin gaske bayan yawaitar sace-sacen mutane a jihohin Neja da Kebbi.
Wasu jihohi, ciki har da Kwara, Filato, Katsina da Nijar, sun kuma rufe makarantu a daidai lokacin da rashin tsaro ke karuwa.
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya kuma umarci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su cire dalibansu daga makaranta nan take.









