Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta ƙara tsaurara aiwatar da dokar bada izinin amfani da baƙin gilashin mota a faɗin ƙasar, daga ranar 2 ga watan Janairu.
Yan sandan jihar Kano sun kama matasa da ake zargi da addabar unguwannin Medile da Guringawa
Hatsarin Mota A Hanyar Madina Ya hallaka ‘Yan Indiya 42
Najeriya ta ƙaryata zargin leken asiri kan jirgin sojinta a Burkina Faso
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar na ƙasa, Benjamin Hundeyin, ya fitar a yammacin ranar Litinin, ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda za su koma manyan hanyoyin ƙasar domin ci gaba da bincike da tabbatar da mallakar izinin amfani da baƙin gilashi ga direbobi.
Sanarwar ta jaddada cewa babu wani hukuncin kotu da ya hana rundunar aiwatar da wannan doka.
Rundunar ta bayyana cewa tsaurara dokar na da nasaba da dalilan tsaro, musamman yadda wasu masu aikata laifuka ke amfani da baƙin gilashin mota wajen taimaka wa ’yan bindiga, safarar makamai da sauran laifuka.
Rundunar ta kuma bayyana cewa daga yanzu zuwa farkon sabuwar shekara, al’umma za su ci gaba da samun damar neman izinin amfani da baƙin gilashin mota ga waɗanda doka ta amince su yi amfani da shi.









