Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bukaci shugabannin Arewa da su tashi tsaye wajen dawo da martabar yankin na Arewa, yana mai gargadin cewa tabarbarewar rashin tsaro da kalubalen tattalin arziki na barazana ga zaman lafiya da ci gaban yankin.
Sakon nasa, wanda Kanal Lawal Gwadabe ya gabatar a wajen taron tunawa da Hassan Katsina karo na biyu, ya jaddada bukatar sabunta manuffofinsu, yayin da yankin ke fama da kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da kuma tsaro.
Babangida ya ƙara da cewa ya kamata ayi koyi daga halayyar janar Hassan wajen aiki da gaskiya da kishin ƙasa, domin samun damar kawar da kalubalen da ke kawo cikas ga ci gaban Arewa na fannoni daban-daban tare da tattalin arzikin Arewacin Najeriya baki daya.
Sannan tsohon shugaban na Najeriya Ya yaba wa waɗanda suka shirya taron saboda nuna sadaukarwar da manyan kasar da suka nuna jajircewa a baya musamman a yanzu da kasarmu ke fama da kalubale masu tarin yawa.









