Home Labarai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jinjina wa sojojin Najeriya kan daƙile yunƙurin...

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jinjina wa sojojin Najeriya kan daƙile yunƙurin juyin mulki a ƙasar Benin

112
0

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba wa “hazaƙa” da dakarun sojin ƙasar suka nuna a ranar Lahadi wajen kare afkuwar juyin mulki a Jamhuriyar Benin wacce suke maƙwaftaka da ƙasar.

A wata sanarwa da shugaban ƙasar ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labarai Bayo Onanuga, Tinubu ya ce “sojojin sun aiki da kwarewa wajen mayar da martani kan buƙatar da gwamnatin Benin ta ceto dimokuraɗiyyar ta shekara 35.”

Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya ɗauki mataki bayan samun buƙatar neman ɗauki biyu.

“Da farko Tinubu ya bayar da umarnin tura jiragen yaƙin Najeriya waɗanda suka karɓe iko da sararin samaniyar Jamhuriyar Benin domin taimakawa wajen kawar da masu iƙirarin juyin mulki daga ginin gidan talabijin na ƙasar da kuma wani sansanin soji,” in ji sanarwar.

“A buƙata ta biyu kuma mahukuntan Benin sun buƙaci yin amfani da kayan aikin rundunar sojin sama ta Najeriya wajen tattara bayanai da kai ɗaukin gaggawa bisa jagorancin hukumomin Benin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 5   +   1   =