Home Labarai Rundunar ‘Yan Sanda:Mun Tsaurara Tsaro A Kan Iyayokin Kano

Rundunar ‘Yan Sanda:Mun Tsaurara Tsaro A Kan Iyayokin Kano

102
0

‎Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tsaurara tsaro a kan iyakokin jihar bayan wani taron bitar dabarun yaki da ta’addanci.

‎A cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a madadin Kwamishinan ‘yan sanda, ya ce CP Bakori ya yaba wa jami’an kan jajircewa da kuma hidimar da suke yi wa rundunar da kuma al’ummar jihar Kano.

‎Kwamishinan ya bayyana cewa, zaman bitar ya yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Egbetokun, musamman kan karfafawa jami’an rundunar.

‎CP Bakori ya umurci Kwamandojin da su zurfafa wayar da kan jama’a a yankunan karkara da birane domin sanar da su irin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 0   +   5   =