Home Labarai NUJ-Ta kafa kwamitin tantancewa da sabunta rijistar mambobi

NUJ-Ta kafa kwamitin tantancewa da sabunta rijistar mambobi

192
0

Kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta kafa kwamitin tantancewa da sabunta rijistar mambobi, bisa umarnin da Babban Ofishin Ƙasa ya bayar.

Wannan na biyo bayan ƙaddamar da shafin rajista na ƙasa, domin tabbatar da inganta adana bayanan ‘yan jarida a fadin ƙasar nan.

A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Sakatare na kungiyar reshen Jihar Jigawa, Comrade Aminu Umar Shuwajo ya fitar, kungiyar ta bayyana cewa aikin sake tantancewar na da nufin ƙoƙarin uwar kungiyar ta ƙasa na tallafawa wajen sabunta bayanan ‘yan jarida a dukkan ƙungiyoyin jihohi da Babban Birnin Tarayya.

Kwamitin ya ƙunshi Auwal Muhammad Kazaure na gidan talabijin ta kasa (NTA) a matsayin shugaban kwamitin, yayin da membobin kwamatin suka hadarda Garba Yakubu na Freedom Radio Dutse, Umar Akilu Majeri na kungiyar ‘yan Jaridu baki dake jihar, Bushira Muhammad Yakasai ta FRCN Horizon FM Dutse, Sani Muhammad Gumel na Radio Jigawa, da Alhassan Aliyu na gidan Talabijin din jihar Jigawa.

Muhammad Umar Hadejia na kungiyar ‘yan Jaridu reshen ma’aikatar watsa labarai ta jiha a matsayin sakataren kwamatin.

Kungiyar ta bayyana cewa an samar da wannan shiri ne domin ƙarfafa ƙwarewar aikin jarida ta hanyar tattara sahihan bayanan ‘yan jarida a Jihar Jigawa, haka kuma kwamatin ba shi da wata manufa na musguna wa kowane Dan Jarida dake jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   9   =