Jamhuriyar Nijar ta dakatar da bai wa ‘yan Amurka bizar shiga ƙasarta
Domin martani ga matakin Amurka na dakatar da bayar da bizar shiga ƙasar ga ‘yan ƙasar Nijar, mahukunta a Yamai sun dakatar da bayar da duk wata biza ga ‘yan ƙasar Amurka, in ji majiyoyin diflomasiyya.
Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun ɗauki matakin mayar da martani ga takwarorinsu na Amurka inda suka dakatar da bayar da biza ga duk wani Ba’amurke da ke son zuwa Nijar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijar ANP ya rawaito majiyoyin diflomasiyya na ƙasar.
An ɗauki matakin ne don bayyana ƙarfin iko da ‘yancin Nijar, kuma diflomasiyyarta ba za ta dinga miƙa kai bori yana hau ga kowace ƙasa ba.”
A ranar Talata 16 ga Disamba ne Amurka ta faɗaɗa ƙarin ƙasashen da ta haramta wa jama’arta shiga Amurka da suka haɗa da ƙasashen ƙawancen Sahel na Mali, Nijar da Burkina Faso.









