Home Labarai Kotun Tarayya Ta Umarci EFCC Ta Gurfanar da Kwamishinan Kuɗin Bauchi Kan...

Kotun Tarayya Ta Umarci EFCC Ta Gurfanar da Kwamishinan Kuɗin Bauchi Kan Zargin Safarar Naira Biliyan 4.6

77
0

[12:27 pm, 26/12/2025] Zaynab Kurawa Premier: Kotun Tarayya da ke Abuja ta umurci Hukumar EFCC da ta gabatar da Kwamishinan Kuɗin Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a ranar 30 ga Disamba domin gurfanar da shi kan zargin safarar kuɗi har Naira biliyan 4.6.
Mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin ne a ranar Laraba, bayan EFCC ta kasa gabatar da Adamu domin karɓar tuhuma karo na biyu a gaban kotu.

EFCC ta zargi Adamu da kamfanin Ayab Agro Products and Freight Company Ltd da haɗa baki wajen safarar N4.65bn tsakanin Yuni da Disamba 2023, lokacin da yake reshen Manajan Polaris Bank a Bauchi, tare da wasu mutane biyu da ake nema ruwa a jallo.
Lauyoyin wanda ake tuhuma sun koka kan ci-gaba da tsare Adamu bace

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta dakatar da duk wani haɗin gwiwar soja da Amurka, biyo bayan rahotannin hare-haren sama da sojojin Amurka suka kai a jihar Sokoto.

Sheikh Gumi ya bayyana cewa shigar Amurka cikin harkokin tsaron Najeriya na iya ƙara tsananta matsalolin tsaro da lalata ikon ƙasa.
Malamin ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na Facebook a ranar Juma’a.

A cewar sa, duk da cewa Musulunci ya halatta yaƙi da ta’addanci, hakan ya kamata ya kasance a hannun masu “tsarkakakkiyar niyya”, yana mai cewa Amurka ba ta da cancantar jagorantar irin wannan yaƙi saboda tarihin ayyukan ta na soja a duniya.
Haka kuma, ya ce shigar Amurka da hujjar kare Kiristoci na iya raba ƙasar ta fuskar addini.
Malamin ya ƙara da cewa hare-haren sama kaɗai ba za su iya kawo ƙarshen ta’addanci ba, yana mai jaddada cewa nasarar yaƙi da ta’addanci na buƙatar ingantattun hare-haren ƙasa, inda ya ce Najeriya na da isassun jami’an tsaro idan aka tsara su yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   10   =