Home Labarai Kayi Murabus Daga Ministan Tsaro Ko Kuma na Maka ka Kotu -Barista...

Kayi Murabus Daga Ministan Tsaro Ko Kuma na Maka ka Kotu -Barista Dantani

310
0

Fitaccen lauya, Barista Hamza Nuhu Dantani, ya shawarci Karamin Ministan Tsaron Najeriya, Bello Matawalle, da ya gaggauta yin murabus ko kuma ya fito bainar Jama’a yayi bayani domin kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa.

Wannan shawara ta biyo bayan yaduwar zargin daya yawaita game da ministan ‘yan tsakanin nan Musamman a kafafen sada zumunta, inda ake danganta ministan da daukar nauyin ’yan ta’adda. zargi da ya jawo mahawara mai zafi a cikin al’umma.

A cikin wani rubutu da Barista Dantani ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce:

“Ina ba da shawara ga Karamin Ministan Tsaro: ko dai ya gaggauta yin murabus domin wanke kansa daga wadannan zarge-zargen, ko kuma na maka shi kotu domin ya yiwa jama’a karin haske game da abin da ake tuhumarsa da shi.”

Dantani ya kara da cewa, daukar ɗaya daga cikin wadannan matakan zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya tare da kawar da shakku a zukatan ’yan kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 10   +   4   =