Fiye da makwanni 2 bayan garkuwa da su da ƴan bindiga suka yi, har yanzu babu labarin fiye da ɗalibai 250 na makarantar kwanan ɗalibai ta St Mary Catholic da ke garin Papiri a jihar Neja.
Shin ko murabus din Badaru ya yi zai kawo karshen matsalar Tsaro a Najeriya
Shin ko murabus din Badaru ya yi zai kawo karshen matsalar Tsaro a Najeriya
Jami’an Tsaro suyi aikisu ba tare jiran umarni ba ~ Christopher Musa
Ɗimbin iyayen waɗannan ɗalibai ne ke ci gaba da nuna ɓacin ransu game da rashin ceto ƴaƴan nasu da ɓatagarin suka sace tun da asubahin ranar 21 ga watan Nuwamban da ya gabata.
Kamar yadda Makarantar ta sanar kwana guda bayan wannan sata, 50 daga cikin ɗaliban sun kuɓuta sai dai tun daga wannan lokaci ba a sake jin ɗuriyar halin da ake ciki da kuma makomar ɗaliban ba.
Wannan garkuwa ta ranar 21 ga watan Nuwamban 2025 na matsayin mai ƙunshe da ɗalibai mafiya yawa tun bayan ɗaliban sakandiren ƴan mata ta Chibok da Boko Haram ta sace a shekarar 2014 wanda a wancan lokaci aka bayyana adadinsu da 276.
Jami’an tsaro dai na ci gaba da nanata cewa, suna aiki tuƙuru wajen ganin sun ceto ɗaliban sai dai a kowacce rana fatan da iyaye ke da shi na sake ganin ƴaƴansu na ci gaba da dusashewa.
Daga shekarar 2014 kawo yanzu wasu alƙaluman sun cewa anyi garkuwa da ɗaliban Najeriya aƙalla dubu 1 da 799 a lokuta daban-daban kodayake an yi nasarar ceto wasu.








